A wata takarda da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar shugaban ya siffanta harin a matsayin halin mugunta
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tir da harin da wasu yan kunar nakin wake suka kai masallaci ranar talata a garin Mubi.
Harin wanda ya faru a safiyar ranar talata yayin da masallata ke sallar asuba yayi sandiyar kashe mutane 50 tare da jikata mutane da dama.
Mutum 50 sun mutu sakamakon harin da yan kunar bakin wake suka kai a wata masallaci dake garin Mubi
A wata takarda da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar shugaban ya siffanta harin a matsayin halin mugunta.
Shugaban ya jajanta ma iyalen wadanda harin ya shafa da al'ummar jihar har ma da gwamnatin jihar, kana yana mai tabbatar masu cewa duk wani mataki da ya kamata a ɗauka wajen kare rayukan mutane daga ta'adancin Boko Haram,gwamnatin sa ta shirya ɗaukawa.
A takarda da Shehu ya fitar, shugaba yayi kira ga al'ummar yankin da su kasance suna masu lura da abubuwan dake faruwa a yankunan su kuma su tabbatar sun kai kara ga jami'an tsaro idan sun ci karo da duk wani abun zargi.
Shugaban ya kara da cewa an bada umarni na tura dakarun rundunar yan sanda yankin tare da jihar Zamfara domin magance ta'adanci.
karanta labarin Barayin shanu sun kai hari karamar hukumar Shinkafi, mutum 50 ne suka rasu sakamakon harin
Kakakin yace shugaba Buhari yana ma iyalen wadanda harin Mubi da na Zamfara ya shafa jaje. Yayi addua'a Allah ya baiwa iyalin hakurin jure rashin da suka samu kana Allah yayi masu rahama.
from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online
No comments:
Post a Comment